Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Bahram Qasemi ya bayyana kalaman da Trump ya yi a kan Iran a lokacin ziyararsa a Paris da cewa Trump ya kara tabbatar da cewa ba shi da masu ba shi shawara da suka san siyasa.
Qasemi ya ce Iran ce ta fara yaki da ayyukan ta’addanci a yankin gabas ta tsakiya, domin kuwa tun daga lokacin samun nasarar juyin Islama kasar take fuskantar ayyukan ta’addanci.
Ya kara da cewa, zargin Iran da taimaka wa ‘yan ta’adda a yankin gabas ta tsakiya da Trump ya yi a bin ban dariya ne ga duk wanda ya ji hakan, domin kuwa Iran ita ce kasar da ta zama karfen kafa ga ‘yan ta’adda a yankin da kuma kasashen da suka kirkiro su, duk kuwa da irin goyon bayan da Amurka take baiwa wadannan kasashe saboda maslharta ta siyasa da tattalin arziki.288